Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,

  2. wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?

  3. Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;

  4. ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.

  5. Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.

  6. Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,

  7. Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.

  8. Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;

  9. duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.

  10. Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,

  11. ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

  12. Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,

  13. wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

  14. Waƙar haurawa. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.

  15. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.

  16. Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?

  17. Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.

  18. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!

  19. Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.

  20. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

  21. Waƙar haurawa. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?

  22. Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

  23. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

  24. tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

  25. Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;