Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.

  2. Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.

  3. Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.

  4. Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.

  5. Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.

  6. Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.

  7. Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.

  8. Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.

  9. Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.

  10. Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.

  11. Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.

  12. Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

  13. ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.

  14. Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada.

  15. Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.

  16. Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

  17. Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada.

  18. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

  19. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

  20. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.

  21. Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.

  22. Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.

  23. Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.

  24. Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.

  25. Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai