Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms: For God's mercies to individuals

58 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da For God's mercies to individuals

  1. Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

  2. Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.

  3. Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

  4. Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.

  5. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.

  6. Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”

  7. Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.

  8. A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.

  9. “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?

  10. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”

  11. Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

  12. don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

  13. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce. Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

  14. Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.

  15. Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

  16. Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

  17. Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

  18. Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

  19. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

  20. A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.

  21. Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

  22. wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

  23. Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.

  24. Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.

  25. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.