Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms: Of Isaiah

6 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Of Isaiah

  1. A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.

  2. Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”

  3. Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.

  4. A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

  5. Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

  6. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”