Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms: Psalms of Affliction

315 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Psalms of Affliction

  1. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!

  2. Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela

  3. Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

  4. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

  5. Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

  6. Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

  7. Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.

  8. Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.

  10. Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela

  11. Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.

  12. Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela

  13. Ku miƙa hadayun da suka dace ku kuma dogara ga Ubangiji.

  14. Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.

  15. Ka cika zuciyata da farin ciki sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.

  16. Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  17. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda. Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata.

  18. Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a.

  19. Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya.

  20. Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne; gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

  21. Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

  22. Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama.

  23. Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma, zan shiga gidanka; da bangirma zan durƙusa ga haikalinka.

  24. Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana.

  25. Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya.