Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms: Psalms of Praise

178 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Psalms of Praise

  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.

  2. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

  3. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

  4. wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?

  5. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

  6. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

  7. dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,

  8. tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

  9. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

  10. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

  11. Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani.

  12. Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su.

  13. Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

  14. wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.

  15. Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

  16. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.

  17. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.

  18. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  19. Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki.

  20. Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma.

  21. Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.

  22. Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye.

  23. Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.

  24. Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;

  25. gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.