Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms: Prophetic Psalms

49 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Prophetic Psalms

  1. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?

  2. Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.

  3. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”

  4. Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

  5. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,

  6. “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”

  7. Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka.

  8. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.

  9. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”

  10. Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.

  11. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.

  12. Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

  13. Miktam ne na Dawuda. Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka.

  14. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

  15. Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.

  16. Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina.

  17. Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona,

  18. Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

  19. Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

  20. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

  21. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,

  22. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  23. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  24. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.

  25. Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.