Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;

  2. za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.

  3. Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.

  4. Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.

  5. Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.

  6. Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.

  7. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.

  8. Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.

  9. Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!

  10. Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.

  11. Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli.

  12. Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.

  13. An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.

  14. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki.

  15. Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza.

  16. Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.

  17. Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne.

  18. Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai.

  19. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne.

  20. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.

  21. Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.

  22. Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.

  23. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.

  24. Ta Dawuda. Zabura ce. Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.

  25. Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi