Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba.

  2. Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

  3. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

  4. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

  5. Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

  6. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

  7. Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.

  8. Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.

  9. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.

  10. Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.

  11. A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.

  12. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

  13. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.

  14. Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta.

  15. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

  16. Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?

  17. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

  18. Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

  19. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.

  20. Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”

  21. Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

  22. Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.

  23. Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

  24. Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

  25. Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.