Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.

  2. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;

  3. Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.

  4. Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

  5. Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

  6. An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

  7. A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

  8. A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.

  9. Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

  10. Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”

  11. Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

  12. Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

  13. Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

  14. Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.

  15. Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.

  16. Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.

  17. Waƙar haurawa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

  18. Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.

  19. Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta.

  20. Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

  21. Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  22. Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.

  23. Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

  24. ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.

  25. Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.