Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.

  2. Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!

  3. Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa.

  4. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.

  5. Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.

  6. Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji.

  7. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.

  8. A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

  9. A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu,

  10. gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”

  11. Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa?

  12. In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa.

  13. Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba.

  14. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!”

  15. Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana,

  16. shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.

  17. Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo.

  18. Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka.

  19. Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.

  20. Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka.

  21. Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.

  22. Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai.

  23. Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni.

  24. Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

  25. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici,