Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Persecution

270 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.

  2. Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.”

  3. Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.

  4. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”

  5. Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe!

  6. Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki.

  7. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”

  8. Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce.

  9. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  10. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi.

  11. Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”

  12. Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”

  13. Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi.

  14. Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”

  15. Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!”

  16. Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel.

  17. Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun mai mulkin Isra’ila da sandar ƙarfe.

  18. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne.

  19. Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”

  20. Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

  21. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.

  22. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  23. Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābankukuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,

  24. Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.

  25. Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”