Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul

619 ayoyi · 103 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske.

  2. Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa.

  3. Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.

  4. Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus.

  5. Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.

  6. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.

  7. Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya.

  8. Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa.

  9. Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.

  10. Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.

  11. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.

  12. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.

  13. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

  14. “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina.

  15. Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.

  16. Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.

  17. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

  18. Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba.

  19. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai.

  20. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

  21. “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.

  22. Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba.

  23. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina.

  24. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

  25. Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a.