Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul

619 ayoyi · 103 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.”

  2. Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”

  3. Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu.

  4. Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci.

  5. Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.

  6. Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.

  7. Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus.

  8. Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.

  9. Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,

  10. har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

  11. Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.”

  12. ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.

  13. Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”

  14. Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.

  15. Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.

  16. Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu.

  17. Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin.

  18. Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.

  19. Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.”

  20. Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.

  21. Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar.

  22. Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.

  23. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a.

  24. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.

  25. Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”