Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables

452 ayoyi · 74 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’

  2. Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.”

  3. Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa.

  4. Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’ ”

  5. Amma Yehowash sarkin Isra’ila ya mai da martani wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ’yar ƙaya a kurmin Lebanon ta aika da saƙo wurin itacen al’ul a Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Amma wani naman jeji ya zo ya tattake ƙayar.

  6. Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.

  7. Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.

  8. Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.

  9. Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.

  10. Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?

  11. Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.

  12. Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,

  13. saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.

  14. An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.

  15. Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi.

  16. Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.

  17. “Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.

  18. Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?

  19. Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.

  20. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”

  21. Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.

  22. A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce

  23. Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.

  24. Ku saurara ku kuma ji muryata; ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.

  25. Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?