Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da All Christians Should Be As Missionaries

198 ayoyi · 66 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

  2. Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.

  3. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

  4. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,

  5. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.

  6. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”

  7. Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.

  8. Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

  9. Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.

  10. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  11. kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

  12. I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

  13. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.

  14. Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;

  15. gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.

  16. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

  17. Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.

  18. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

  19. Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.

  20. Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

  21. Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.

  22. Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.

  23. aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

  24. Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba.

  25. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.