Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da All Christians Should Be As Missionaries

198 ayoyi · 66 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu,

  2. su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  3. Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,

  4. zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

  5. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

  6. Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,

  7. domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.

  8. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.

  9. Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.

  10. Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.

  11. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.

  12. Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.

  13. Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  14. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  15. ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

  16. sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  17. Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  18. Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

  19. Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba

  20. Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,

  21. Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.

  22. In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.

  23. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah.