Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da All Christians Should Be As Missionaries: Philemon

6 ayoyi · 66 fannoni

Ayoyi game da Philemon

  1. Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,

  2. zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

  3. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

  4. Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,

  5. domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.

  6. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.