Tsallake zuwa abun ciki

Aquila

6 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Aquila

  1. A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,

  2. Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.

  3. Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.

  4. Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.

  5. Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.

  6. Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus.