Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da All Christians Should Be As Missionaries: In declaring what God has done for them
Ayoyi game da In declaring what God has done for them
Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.
Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.
Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,
a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.