- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 7:29kusan 31 M.
domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.
- Mattiyu 8:1kusan 31 M.
Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.
- Mattiyu 8:2kusan 31 M.
Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”
- Mattiyu 8:3kusan 31 M.
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
- Mattiyu 8:4kusan 31 M.
Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”
- Mattiyu 8:5kusan 31 M.
Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.
- Mattiyu 8:6kusan 31 M.
Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”
- Mattiyu 8:7kusan 31 M.
Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”
- Mattiyu 8:8kusan 31 M.
Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.
- Mattiyu 8:9kusan 31 M.
Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.”
- Mattiyu 8:10kusan 31 M.
Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba.
- Mattiyu 8:11kusan 31 M.
Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.
- Mattiyu 8:12kusan 31 M.
Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”
- Mattiyu 8:13kusan 31 M.
Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
- Mattiyu 8:14kusan 31 M.
Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.
- Mattiyu 8:15kusan 31 M.
Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
- Mattiyu 8:16kusan 31 M.
Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
- Mattiyu 8:17kusan 31 M.
Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
- Mattiyu 8:18kusan 31 M.
Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.
- Mattiyu 8:19kusan 31 M.
Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”
- Mattiyu 8:20kusan 31 M.
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
- Mattiyu 8:21kusan 31 M.
Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”
- Mattiyu 8:22kusan 31 M.
Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
- Mattiyu 8:23kusan 31 M.
Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
- Mattiyu 8:24kusan 31 M.
Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.