Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 7:4kusan 31 M.

    Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?

  2. Mattiyu 7:5kusan 31 M.

    Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.

  3. Mattiyu 7:6kusan 31 M.

    “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.

  4. Mattiyu 7:7kusan 31 M.

    “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.

  5. Mattiyu 7:8kusan 31 M.

    Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

  6. Mattiyu 7:9kusan 31 M.

    “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse?

  7. Mattiyu 7:10kusan 31 M.

    Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji?

  8. Mattiyu 7:11kusan 31 M.

    In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

  9. Mattiyu 7:12kusan 31 M.

    Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.

  10. Mattiyu 7:13kusan 31 M.

    “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.

  11. Mattiyu 7:14kusan 31 M.

    Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.

  12. Mattiyu 7:15kusan 31 M.

    “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne.

  13. Mattiyu 7:16kusan 31 M.

    Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

  14. Mattiyu 7:17kusan 31 M.

    Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  15. Mattiyu 7:18kusan 31 M.

    Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  16. Mattiyu 7:19kusan 31 M.

    Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.

  17. Mattiyu 7:20kusan 31 M.

    Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

  18. Mattiyu 7:21kusan 31 M.

    “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.

  19. Mattiyu 7:22kusan 31 M.

    Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’

  20. Mattiyu 7:23kusan 31 M.

    Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

  21. Mattiyu 7:24kusan 31 M.

    “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

  22. Mattiyu 7:25kusan 31 M.

    Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

  23. Mattiyu 7:26kusan 31 M.

    Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.

  24. Mattiyu 7:27kusan 31 M.

    Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

  25. Mattiyu 7:28kusan 31 M.

    Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,