Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 11:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  2. Firistoci 11:2kusan 1490 K.H.

    “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.

  3. Firistoci 11:3kusan 1490 K.H.

    Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.

  4. Firistoci 11:4kusan 1490 K.H.

    “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.

  5. Firistoci 11:5kusan 1490 K.H.

    Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku.

  6. Firistoci 11:6kusan 1490 K.H.

    Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku.

  7. Firistoci 11:7kusan 1490 K.H.

    Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku.

  8. Firistoci 11:8kusan 1490 K.H.

    Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.

  9. Firistoci 11:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.

  10. Firistoci 11:10kusan 1490 K.H.

    Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.

  11. Firistoci 11:11kusan 1490 K.H.

    Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.

  12. Firistoci 11:12kusan 1490 K.H.

    Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.

  13. Firistoci 11:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,

  14. Firistoci 11:14kusan 1490 K.H.

    shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa,

  15. Firistoci 11:15kusan 1490 K.H.

    kowane irin hankaka,

  16. Firistoci 11:16kusan 1490 K.H.

    mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,

  17. Firistoci 11:17kusan 1490 K.H.

    ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe,

  18. Firistoci 11:18kusan 1490 K.H.

    kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu,

  19. Firistoci 11:19kusan 1490 K.H.

    shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.

  20. Firistoci 11:20kusan 1490 K.H.

    “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.

  21. Firistoci 11:21kusan 1490 K.H.

    Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

  22. Firistoci 11:22kusan 1490 K.H.

    Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.

  23. Firistoci 11:23kusan 1490 K.H.

    Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

  24. Firistoci 11:24kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.

  25. Firistoci 11:25kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.