Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 9:20kusan 1490 K.H.

    suka shimfiɗa waɗannan a kan ƙirjin, sa’an nan Haruna ya ƙone kitsen a kan bagade.

  2. Firistoci 9:21kusan 1490 K.H.

    Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta.

  3. Firistoci 9:22kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka.

  4. Firistoci 9:23kusan 1490 K.H.

    Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane.

  5. Firistoci 9:24kusan 1490 K.H.

    Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.

  6. Firistoci 10:1kusan 1490 K.H.

    ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

  7. Firistoci 10:2kusan 1490 K.H.

    Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.

  8. Firistoci 10:3kusan 1490 K.H.

    Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’ ” Haruna ya yi shiru.

  9. Firistoci 10:4kusan 1490 K.H.

    Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”

  10. Firistoci 10:5kusan 1490 K.H.

    Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.

  11. Firistoci 10:6kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.

  12. Firistoci 10:7kusan 1490 K.H.

    Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa.

  13. Firistoci 10:8kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce,

  14. Firistoci 10:9kusan 1490 K.H.

    “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.

  15. Firistoci 10:10kusan 1490 K.H.

    Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta,

  16. Firistoci 10:11kusan 1490 K.H.

    za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”

  17. Firistoci 10:12kusan 1490 K.H.

    Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.

  18. Firistoci 10:13kusan 1490 K.H.

    Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni.

  19. Firistoci 10:14kusan 1490 K.H.

    Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.

  20. Firistoci 10:15kusan 1490 K.H.

    Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”

  21. Firistoci 10:16kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar, ’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya,

  22. Firistoci 10:17kusan 1490 K.H.

    “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji.

  23. Firistoci 10:18kusan 1490 K.H.

    Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.”

  24. Firistoci 10:19kusan 1490 K.H.

    Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”

  25. Firistoci 10:20kusan 1490 K.H.

    Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu.