Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 11:26kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu.

  2. Firistoci 11:27kusan 1490 K.H.

    Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.

  3. Firistoci 11:28kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.

  4. Firistoci 11:29kusan 1490 K.H.

    “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

  5. Firistoci 11:30kusan 1490 K.H.

    da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

  6. Firistoci 11:31kusan 1490 K.H.

    Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.

  7. Firistoci 11:32kusan 1490 K.H.

    Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.

  8. Firistoci 11:33kusan 1490 K.H.

    In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.

  9. Firistoci 11:34kusan 1490 K.H.

    Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.

  10. Firistoci 11:35kusan 1490 K.H.

    Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.

  11. Firistoci 11:36kusan 1490 K.H.

    Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.

  12. Firistoci 11:37kusan 1490 K.H.

    In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.

  13. Firistoci 11:38kusan 1490 K.H.

    Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.

  14. Firistoci 11:39kusan 1490 K.H.

    “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.

  15. Firistoci 11:40kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  16. Firistoci 11:41kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.

  17. Firistoci 11:42kusan 1490 K.H.

    Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.

  18. Firistoci 11:43kusan 1490 K.H.

    Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.

  19. Firistoci 11:44kusan 1490 K.H.

    Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.

  20. Firistoci 11:45kusan 1490 K.H.

    Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.

  21. Firistoci 11:46kusan 1490 K.H.

    “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.

  22. Firistoci 11:47kusan 1490 K.H.

    Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ”

  23. Firistoci 12:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  24. Firistoci 12:2kusan 1490 K.H.

    “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.

  25. Firistoci 12:3kusan 1490 K.H.

    A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.