- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 12:4kusan 1490 K.H.
Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.
- Firistoci 12:5kusan 1490 K.H.
In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.
- Firistoci 12:6kusan 1490 K.H.
“ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.
- Firistoci 12:7kusan 1490 K.H.
Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace.
- Firistoci 12:8kusan 1490 K.H.
In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ”
- Firistoci 13:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
- Firistoci 13:2kusan 1490 K.H.
“Sa’ad da wani yana da kumburi, ko ɓamɓaroki, ko tabo a fatar jikinsa da zai iya zama cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga Haruna firist, ko kuwa ga ɗaya a cikin ’ya’yansa maza wanda yake firist.
- Firistoci 13:3kusan 1490 K.H.
Firist zai bincika mikin da yake a fatar mai cutar, in gashin a mikin ya juya ya zama fari, mikin kuma ya zama kamar ya fi zurfin fatar jiki, wannan cutar kuturta ce. Sa’ad da firist ya bincike shi, zai furta shi marar tsarki.
- Firistoci 13:4kusan 1490 K.H.
In tabon a fata jikinsa fari ne amma bai zama ya fi zurfin fatar jikin ba, gashin a cikinsa kuma bai juya ya zama fari ba, firist ɗin zai kaɗaice mai cutar na kwana bakwai.
- Firistoci 13:5kusan 1490 K.H.
A rana ta bakwai firist zai bincike shi, in kuwa ya ga cewa mikin bai canja ba, bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, zai kaɗaice shi na waɗansu ƙarin kwana bakwai.
- Firistoci 13:6kusan 1490 K.H.
A rana ta bakwai ɗin firist zai sāke bincike shi, in kuwa mikin ya bushe bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi mai tsarki; ƙurji ne kawai. Dole mutumin yă wanke rigunansa, zai kuma tsarkaka.
- Firistoci 13:7kusan 1490 K.H.
Amma in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa bayan ya nuna kansa ga firist don a furta shi tsarkake, dole yă sāke bayyana a gaban firist.
- Firistoci 13:8kusan 1490 K.H.
Firist ɗin zai bincike shi, in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa, zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa.
- Firistoci 13:9kusan 1490 K.H.
“Sa’ad da wani yana da cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga firist.
- Firistoci 13:10kusan 1490 K.H.
Firist zai bincike shi, in kuwa farin kumburi a fatar jikin ya juyar da gashin fari in kuma akwai sabon miki a kumburi,
- Firistoci 13:11kusan 1490 K.H.
to, cutar fatar jikin ne mai ƙarfi kuma firist zai furta shi marar tsarki. Ba zai kaɗaice shi ba, domin ya riga ya zama marar tsarki.
- Firistoci 13:12kusan 1490 K.H.
“In cutar ta fashe ko’ina a fatar jiki, har iyakar ganin firist, ta rufe dukan fatar jikin mai fama da cutar, daga kai har zuwa ƙafa,
- Firistoci 13:13kusan 1490 K.H.
firist zai bincike shi, in cutar ta riga ta rufe dukan jikinsa, zai furta wannan mutum tsarkakakke ne. Da yake ya juya fari fat, tsarkakakke ne.
- Firistoci 13:14kusan 1490 K.H.
Amma sa’ad da sabon miki ya bayyana a jikinsa, zai furta shi marar tsarki.
- Firistoci 13:15kusan 1490 K.H.
Sa’ad da firist ɗin ya ga sabon miki, zai furta shi marar tsarki. Sabon mikin marar tsarki, yana da cuta mai yaɗuwa.
- Firistoci 13:16kusan 1490 K.H.
A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist.
- Firistoci 13:17kusan 1490 K.H.
Firist zai bincike shi, in kuma mikin ya juya ya zama fari, firist zai furta mai cutar tsarkakakke; to, zai zama tsarkakakke.
- Firistoci 13:18kusan 1490 K.H.
“Sa’ad da wani yana da kumburi a fatar jikinsa ya kuma warke,
- Firistoci 13:19kusan 1490 K.H.
kuma a inda ƙurjin yake, wani farin kumburi ko tabo ja-ja, fari-fari ya bayyana, dole yă gabatar da kansa ga firist.
- Firistoci 13:20kusan 1490 K.H.
Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake.