Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, a nan ma a Yahuda muna jin tsoro, balle mu tafi Keyila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa!”

  2. Dawuda ya sāke nemi nufin Ubangiji, sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka gangara zuwa Keyila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

  3. Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu.

  4. (Abiyatar ɗan Ahimelek ya zo da efod sa’ad da ya gudo zuwa wurin Dawuda a Keyila.)

  5. 1 Sama’ila 23:7kusan 1061 K.H.

    Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya tafi Keyila, sai ya ce, “Allah ya bashe shi a hannuna, domin Dawuda ya kulle kansa ke nan da ya shiga birnin da yake da ƙofofin da ake kulle da ƙarafa.”

  6. 1 Sama’ila 23:8kusan 1061 K.H.

    Shawulu ya kira dukan sojojinsa don yaƙi, su gangaro zuwa Keyila su mamaye Dawuda da mutanensa.

  7. 1 Sama’ila 23:9kusan 1061 K.H.

    Da Dawuda ya ji labari Shawulu yana shirya hanyar da zai kashe shi, sai ya ce wa Abiyatar firist, “Kawo mini efod a nan.”

  8. 1 Sama’ila 23:10kusan 1061 K.H.

    Dawuda ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bawanka ya sami labari cewa tabbatacce Shawulu yana shirin zuwa Keyila yă hallaka garin saboda ni.

  9. 1 Sama’ila 23:11kusan 1061 K.H.

    Mutanen Keyila za su bashe ni a gare shi? Shawulu zai gangaro nan kamar yadda bawanka ya sami labari? Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka gaya wa bawanka.” Ubangiji ya ce, “Zai zo.”

  10. 1 Sama’ila 23:12kusan 1061 K.H.

    Dawuda ya sāke cewa, “Mutanen Keyila za su bashe ni da mutanena ga Shawulu?” Ubangiji ya ce, “Za su yi.”

  11. 1 Sama’ila 23:13kusan 1061 K.H.

    Saboda haka Dawuda da mutanensa wajen mutum ɗari shida suka bar Keyila, suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan. Sa’ad da aka gaya wa Shawulu cewa Dawuda ya tsere daga Keyila, sai ya fasa tafiya can.

  12. 1 Sama’ila 23:14kusan 1061 K.H.

    Dawuda ya zauna a jeji cikin kogunan duwatsu da kuma tuddan jejin Zif. Kowace rana Shawulu ya yi ta neman Dawuda amma Allah bai bashe Dawuda a hannunsa ba.

  13. 1 Sama’ila 23:15kusan 1061 K.H.

    A lokacin da Dawuda yana zaune a Horesh cikin jejin Zif, ya sami labari cewa Shawulu ya fito don yă kashe shi.

  14. 1 Sama’ila 23:16kusan 1061 K.H.

    Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah.

  15. 1 Sama’ila 23:17kusan 1061 K.H.

    Ya ce, “Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka.”

  16. 1 Sama’ila 23:18kusan 1061 K.H.

    Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.

  17. 1 Sama’ila 23:19kusan 1061 K.H.

    Zifawa suka tafi wurin Shawulu a Gibeya suka ce masa, “Ashe, ba Dawuda ne yake ɓuya a cikinmu a kogwannin duwatsu a Horesh a bisan tudun Hakila, kudu da Yeshimon ba?

  18. 1 Sama’ila 23:20kusan 1061 K.H.

    Yanzu, ya sarki, ka gangaro, ka zo a duk lokacin da ka ga ya yi maka, ka zo mu kuma hakkinmu ne mu bashe shi a hannun sarki.”

  19. 1 Sama’ila 23:21kusan 1061 K.H.

    Shawulu ya ce, “Ubangiji ya yi muku albarka, gama kun damu da ni.

  20. 1 Sama’ila 23:22kusan 1061 K.H.

    Ku tafi ku ƙara shiri. Ku san inda yakan tafi, wane ne kuma ya gan shi a can. An gaya mini cewa shi mai wayo ne sosai.

  21. 1 Sama’ila 23:23kusan 1061 K.H.

    Ku binciko duk wuraren da yakan ɓuya, sai ku dawo ku gaya mini tabbataccen labari. Sa’an nan zan tafi tare da ku in yana can. Zan nemi shi ko’ina cikin dukan kabilar Yahuda.”

  22. 1 Sama’ila 23:24kusan 1061 K.H.

    Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon.

  23. 1 Sama’ila 23:25kusan 1061 K.H.

    Shawulu da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya gangara cikin duwatsu ya zauna a cikin jejin Mawon. Sa’ad da Shawulu ya ji haka, sai ya tafi jejin Mawon yana fafaran Dawuda.

  24. 1 Sama’ila 23:26kusan 1061 K.H.

    Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su,

  25. 1 Sama’ila 23:27kusan 1061 K.H.

    sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”