Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 20:33kusan 1062 K.H.

    Amma Shawulu ya jefe shi da māshi don yă kashe shi. A nan ne Yonatan ya san lalle mahaifinsa ya yi niyya yă kashe Dawuda.

  2. 1 Sama’ila 20:34kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda.

  3. 1 Sama’ila 20:35kusan 1062 K.H.

    Da safe Yonatan ya tafi domin yă sadu da Dawuda a fili. Ya tafi tare da wani ƙaramin yaro.

  4. 1 Sama’ila 20:36kusan 1062 K.H.

    Ya ce wa yaron, “Yi ruga da gudu ka nemo kibiyoyin da na harba.” Da yaron ya ruga sai ya harba kibiya a gaba da shi.

  5. 1 Sama’ila 20:37kusan 1062 K.H.

    Da yaron ya isa wurin da kibiyan Yonatan ya fāɗi, Yonatan ya kira shi ya ce, “Kibiyan na gabanka fa.”

  6. 1 Sama’ila 20:38kusan 1062 K.H.

    Sai ya tā da murya ya ce, “Maza, yi sauri kada ka tsaya.” Yaron ya ɗauko kibiya ya kawo wa maigidansa.

  7. 1 Sama’ila 20:39kusan 1062 K.H.

    (Yaron kuwa bai san kome game da wannan abu ba, sai Yonatan da Dawuda kawai.)

  8. 1 Sama’ila 20:40kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ba wa yaron makaman ya ce, “Ka ɗauka ka koma gari.”

  9. 1 Sama’ila 20:41kusan 1062 K.H.

    Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai.

  10. 1 Sama’ila 20:42kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.

  11. 1 Sama’ila 21:1kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”

  12. 1 Sama’ila 21:2kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni.

  13. 1 Sama’ila 21:3kusan 1062 K.H.

    Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.”

  14. 1 Sama’ila 21:4kusan 1062 K.H.

    Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”

  15. 1 Sama’ila 21:5kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”

  16. 1 Sama’ila 21:6kusan 1062 K.H.

    Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.

  17. 1 Sama’ila 21:7kusan 1062 K.H.

    A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.

  18. 1 Sama’ila 21:8kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya ce wa Ahimelek, “Ba ka da māshi ko takobi a nan? Ban kawo māshina ko wani makami ba gama saƙon sarki ya zo mini da gaggawa.”

  19. 1 Sama’ila 21:9kusan 1062 K.H.

    Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”

  20. 1 Sama’ila 21:10kusan 1062 K.H.

    A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat.

  21. 1 Sama’ila 21:11kusan 1062 K.H.

    Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa, “Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”

  22. 1 Sama’ila 21:12kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai.

  23. 1 Sama’ila 21:13kusan 1062 K.H.

    Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa.

  24. 1 Sama’ila 21:14kusan 1062 K.H.

    Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina?

  25. 1 Sama’ila 21:15kusan 1062 K.H.

    Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?”