Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 20:8kusan 1062 K.H.

    Kai kuma, ka nuna alheri ga bawanka, gama ka riga ka yi yarjejjeniya da ni a gaban Ubangiji, in kuwa na yi laifi ne sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bashe ni ga mahaifinka?”

  2. 1 Sama’ila 20:9kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ce, “Labudda! In na ji ƙishin-ƙishin, cewa mahaifina yana neman yă kashe ka ashe, ba zan gaya maka ba?”

  3. 1 Sama’ila 20:10kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya ce, “Wa zai gaya mini idan mahaifinka ya amsa maka da amsa marar daɗi?”

  4. 1 Sama’ila 20:11kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ce, “Zo mu fita zuwa fili.” Sai suka tafi tare.

  5. 1 Sama’ila 20:12kusan 1062 K.H.

    Sai Yonatan ya ce wa Dawuda, “Na yi rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila cewa war haka jibi, zan yi ƙoƙari in ji daga mahaifina, idan ya yi magana mai kyau game da kai, zan gaya maka.

  6. 1 Sama’ila 20:13kusan 1062 K.H.

    Amma in mahaifina ya sa zuciya yă cuce ka, Ubangiji yă hukunta ni da hukunci mai tsanani in ban gaya maka ba, in kuma sa ka ka tafi lafiya. Ubangiji yă kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.

  7. 1 Sama’ila 20:14kusan 1062 K.H.

    Amma ka nuna mini alheri marar ƙarewa iri ta Ubangiji dukan rayuwata don kada a kashe ni.

  8. 1 Sama’ila 20:15kusan 1062 K.H.

    Kada kuma ka yanke alherinka ga iyalina ko da Ubangiji ya hallaka dukan maƙiyin Dawuda a duniya.”

  9. 1 Sama’ila 20:16kusan 1062 K.H.

    Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji yă kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa.

  10. 1 Sama’ila 20:17kusan 1062 K.H.

    Yonatan kuwa ya sa Dawuda ya sāke tabbatar masa rantsuwansa game da abokantakarsa da shi, gama yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.

  11. 1 Sama’ila 20:18kusan 1062 K.H.

    Sai Yonatan ya gaya wa Dawuda cewa, “Gobe ne Bikin Sabon Wata, za a rasa ka, da yake kujerarka za tă kasance ba kowa a kai.

  12. 1 Sama’ila 20:19kusan 1062 K.H.

    Jibi wajajen yamma, ka tafi wurin da ka ɓuya lokacin da wannan matsala ta fara, ka tsaya kusa da dutsen Etsel.

  13. 1 Sama’ila 20:20kusan 1062 K.H.

    Zan harbi kibiya uku ta wajen, sai ka ce dai ina harbin baka.

  14. 1 Sama’ila 20:21kusan 1062 K.H.

    Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari.

  15. 1 Sama’ila 20:22kusan 1062 K.H.

    Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka.

  16. 1 Sama’ila 20:23kusan 1062 K.H.

    Game da al’amarin da muka tattauna da ni da kai kuwa, ka tuna fa Ubangiji ne shaida tsakanina da kai har abada.”

  17. 1 Sama’ila 20:24kusan 1062 K.H.

    Dawuda ya tafi ya ɓuya a fili. Sa’ad da ranar Bikin Sabon Wata ta zo, sarki ya zauna don yă ci.

  18. 1 Sama’ila 20:25kusan 1062 K.H.

    Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa.

  19. 1 Sama’ila 20:26kusan 1062 K.H.

    Shawulu bai ce kome ba a ranar domin ya yi tsammani wataƙila wani abu ya faru da Dawuda ya mai da shi marar tsarki, tabbatacce ba shi da tsarki.

  20. 1 Sama’ila 20:27kusan 1062 K.H.

    Amma kashegari, rana ta biyu ga wata, kujeran Dawuda kuma ba kowa, sai Shawulu ya ce wa ɗansa Yonatan, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo cin abinci, jiya da yau ba?”

  21. 1 Sama’ila 20:28kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ce, “Dawuda ya nemi izinina don yă tafi Betlehem.

  22. 1 Sama’ila 20:29kusan 1062 K.H.

    Ya ce, ‘Bari in tafi gama iyalinmu suna miƙa hadaya a gari, ’yan’uwana kuwa sun gayyace ni in kasance a can. In na sami yardarka, bari in tafi in ga ’yan’uwana.’ Dalilin ke nan da bai zo ci da sarki ba.”

  23. 1 Sama’ila 20:30kusan 1062 K.H.

    Fushin Shawulu ya ƙuna a kan Yonatan, sai ya ce masa, “Kai shege ne, haihuwar banzan mace; ai, na san kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulaƙantar da kanka da mahaifinka.

  24. 1 Sama’ila 20:31kusan 1062 K.H.

    Muddin ɗan Yesse yana da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za tă kahu ba. Yanzu sai ka je ka kawo mini shi. Dole yă mutu.”

  25. 1 Sama’ila 20:32kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa zai mutu? Me ya yi?”