Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 31:4kusan 1056 K.H.

    Sai Shawulu ya ce wa mai ɗauka masa makami, “Ka zare takobinka ka soke ni, kada waɗannan marasa kaciya su zo su ci mini mutunci, su kashe ni.” Amma mai ɗaukan makaman bai yarda ba don ya ji tsoro sosai. Sai Shawulu ya zāre takobinsa ya soki kansa.

  2. 1 Sama’ila 31:5kusan 1056 K.H.

    Da mai ɗaukar makamai ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya zāre takobinsa ya soki kansa ya mutu.

  3. 1 Sama’ila 31:6kusan 1056 K.H.

    Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya.

  4. 1 Sama’ila 31:7kusan 1056 K.H.

    Sa’ad da Isra’ilawa na bakin kwari da waɗanda suke hayin Urdun suka ga sojojin Isra’ila suna gudu, Shawulu da yaransa uku kuma duk sun mutu, sai suka bar mallakansu suka sheƙa da gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka mamaye wuraren.

  5. 1 Sama’ila 31:8kusan 1056 K.H.

    Kashegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka tarar Shawulu da ’ya’yansa uku duk sun mutu, a dutsen Gilbowa.

  6. 1 Sama’ila 31:9kusan 1056 K.H.

    Suka sare kansa suka tuɓe makamansa, suka aika manzanni a dukan ƙasar Filistiyawa, su ba da labarin a haikalin allolinsu da cikin mutanensu.

  7. 1 Sama’ila 31:10kusan 1056 K.H.

    Suka ajiye makaman Shawulu a cikin haikalin gumakan Ashtarot. Suka kafa gawarsa a kan katanga Bet-Shan.

  8. 1 Sama’ila 31:11kusan 1056 K.H.

    Sa’ad da mutanen Yabesh Gileyad suka sami labarin abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu.

  9. 1 Sama’ila 31:12kusan 1056 K.H.

    Sai dukan jarumawansu suka tashi cikin dare suka tafi Bet-Shan suka saukar da gawar Shawulu da na ’ya’yansa daga kan katangan Bet-Shan suka tafi Yabesh inda suka ƙone su.

  10. 1 Sama’ila 31:13kusan 1056 K.H.

    Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.