Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 18:12kusan 1063 K.H.

    Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.

  2. 1 Sama’ila 18:13kusan 1063 K.H.

    Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su.

  3. 1 Sama’ila 18:14kusan 1063 K.H.

    A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi.

  4. 1 Sama’ila 18:15kusan 1063 K.H.

    Da Shawulu ya ga yadda yake cin nasara, sai ya ji tsoronsa.

  5. 1 Sama’ila 18:16kusan 1063 K.H.

    Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu.

  6. 1 Sama’ila 18:17kusan 1063 K.H.

    Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”

  7. 1 Sama’ila 18:18kusan 1063 K.H.

    Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Wane ni, wa ya san iyayena ko kabilar iyayena a Isra’ila da zan zama surukin sarki?”

  8. 1 Sama’ila 18:19kusan 1063 K.H.

    Da lokaci ya kai da Merab ’yar Shawulu za tă yi aure da Dawuda, sai aka aurar da ita wa Adriyel na Mehola.

  9. 1 Sama’ila 18:20kusan 1063 K.H.

    Mikal ’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce,

  10. 1 Sama’ila 18:21kusan 1063 K.H.

    “Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”

  11. 1 Sama’ila 18:22kusan 1063 K.H.

    Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ”

  12. 1 Sama’ila 18:23kusan 1063 K.H.

    Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.”

  13. 1 Sama’ila 18:24kusan 1063 K.H.

    Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa.

  14. 1 Sama’ila 18:25kusan 1063 K.H.

    Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.

  15. 1 Sama’ila 18:26kusan 1063 K.H.

    Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika,

  16. 1 Sama’ila 18:27kusan 1063 K.H.

    Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.

  17. 1 Sama’ila 18:28kusan 1063 K.H.

    Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,

  18. 1 Sama’ila 18:29kusan 1063 K.H.

    sai Shawulu ya ƙara jin tsoron Dawuda har ya zama maƙiyinsa a dukan sauran rayuwarsa.

  19. 1 Sama’ila 18:30kusan 1063 K.H.

    Manyan sojojin Filistiyawa suka yi ta fita suna yaƙi da Isra’ilawa, amma kullum Dawuda yakan sami nasara fiye da sauran manyan sojojin Shawulu. Ta haka ya yi suna ƙwarai.

  20. 1 Sama’ila 19:1kusan 1062 K.H.

    Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai.

  21. 1 Sama’ila 19:2kusan 1062 K.H.

    Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya.

  22. 1 Sama’ila 19:3kusan 1062 K.H.

    Zan je in tsaya da mahaifina a fili inda kake, zan yi masa magana game da kai. Zan kuma gaya maka abin da na ji.”

  23. 1 Sama’ila 19:4kusan 1062 K.H.

    Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske.

  24. 1 Sama’ila 19:5kusan 1062 K.H.

    Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”

  25. 1 Sama’ila 19:6kusan 1062 K.H.

    Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.”