Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 17:20kusan 1063 K.H.

    Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.

  2. 1 Sama’ila 17:21kusan 1063 K.H.

    Isra’ila da Filistiyawa suka ja dāgā suna fuskantar junansu.

  3. 1 Sama’ila 17:22kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa.

  4. 1 Sama’ila 17:23kusan 1063 K.H.

    Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi.

  5. 1 Sama’ila 17:24kusan 1063 K.H.

    Da Isra’ilawa suka ga mutumin, sai dukansu suka gudu saboda tsananin tsoro.

  6. 1 Sama’ila 17:25kusan 1063 K.H.

    Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”

  7. 1 Sama’ila 17:26kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”

  8. 1 Sama’ila 17:27kusan 1063 K.H.

    Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.”

  9. 1 Sama’ila 17:28kusan 1063 K.H.

    Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”

  10. 1 Sama’ila 17:29kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?”

  11. 1 Sama’ila 17:30kusan 1063 K.H.

    Sai ya juya wajen wani kuma ya sāke kawo zancen, mutanen kuwa suka amsa masa kamar dā.

  12. 1 Sama’ila 17:31kusan 1063 K.H.

    Aka ji abin da Dawuda ya ce, aka kuwa gaya wa Shawulu, Shawulu kuma ya aika a kawo shi.

  13. 1 Sama’ila 17:32kusan 1063 K.H.

    Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”

  14. 1 Sama’ila 17:33kusan 1063 K.H.

    Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”

  15. 1 Sama’ila 17:34kusan 1063 K.H.

    Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.

  16. 1 Sama’ila 17:35kusan 1063 K.H.

    Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe.

  17. 1 Sama’ila 17:36kusan 1063 K.H.

    Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.

  18. 1 Sama’ila 17:37kusan 1063 K.H.

    Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  19. 1 Sama’ila 17:38kusan 1063 K.H.

    Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.

  20. 1 Sama’ila 17:39kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su.

  21. 1 Sama’ila 17:40kusan 1063 K.H.

    Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin.

  22. 1 Sama’ila 17:41kusan 1063 K.H.

    Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.

  23. 1 Sama’ila 17:42kusan 1063 K.H.

    Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi.

  24. 1 Sama’ila 17:43kusan 1063 K.H.

    Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.

  25. 1 Sama’ila 17:44kusan 1063 K.H.

    Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”