Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 16:18kusan 1063 K.H.

    Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”

  2. 1 Sama’ila 16:19kusan 1063 K.H.

    Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.”

  3. 1 Sama’ila 16:20kusan 1063 K.H.

    Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.

  4. 1 Sama’ila 16:21kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke.

  5. 1 Sama’ila 16:22kusan 1063 K.H.

    Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.”

  6. 1 Sama’ila 16:23kusan 1063 K.H.

    Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.

  7. 1 Sama’ila 17:1kusan 1063 K.H.

    To, fa, Filistiyawa suka tattara mayaƙansu suka haɗu a Soko cikin Yahuda domin yaƙi. Suka yi sansani a Efes-Dammim, tsakanin Soko da Azeka.

  8. 1 Sama’ila 17:2kusan 1063 K.H.

    Shawulu da Isra’ilawa suka taru suka yi sansani a Kwarin Ela suka ja dāgā don su yi yaƙi da Filistiyawa.

  9. 1 Sama’ila 17:3kusan 1063 K.H.

    Filistiyawa suka zauna a tudu guda, Isra’ilawa kuma suka zauna a ɗaya tudun. Kwari yana a tsakaninsu.

  10. 1 Sama’ila 17:4kusan 1063 K.H.

    Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara.

  11. 1 Sama’ila 17:5kusan 1063 K.H.

    Ya sa hular kwanon da aka yi da tagulla, da rigar ƙarfe mai sulke, nauyin rigar ya kai shekel dubu biyar.

  12. 1 Sama’ila 17:6kusan 1063 K.H.

    A ƙafafunsa kuwa ya sa ƙarafar tagulla, rataye a bayansa kuma māshi ne na tagulla.

  13. 1 Sama’ila 17:7kusan 1063 K.H.

    Ƙotar kibiyarsa kuwa kamar sandar saƙar igiya take, ƙarfen kibiyar kuma nauyinsa ya kai shekel ɗari shida. Mai riƙe masa garkuwa yana tafe a gabansa.

  14. 1 Sama’ila 17:8kusan 1063 K.H.

    Goliyat ya tsaya ya tā da murya wa hafsoshin Isra’ila ya ce, “Me ya sa kuka fito kuna layi don yaƙi? Ni ba Bafilistin ba ne? Ku kuma ba bayin Shawulu ba ne? Ku zaɓi waninku yă zo nan.

  15. 1 Sama’ila 17:9kusan 1063 K.H.

    In zai iya yin faɗa har yă kashe ni, to, za mu zama bayinku. Amma in na fi ƙarfinsa na kashe shi, to, sai ku zama bayinmu, ku kuma yi mana bauta.”

  16. 1 Sama’ila 17:10kusan 1063 K.H.

    Sai Bafilistin ya ce, “A wannan rana, na kalubalanci sojojin Isra’ila, ku ba ni mutum ɗaya mu yi faɗa.”

  17. 1 Sama’ila 17:11kusan 1063 K.H.

    Da jin maganganun Bafilistin, sai Shawulu da dukan Isra’ila suka damu suka kuma ji tsoro.

  18. 1 Sama’ila 17:12kusan 1063 K.H.

    To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.

  19. 1 Sama’ila 17:13kusan 1063 K.H.

    Manyan ’ya’yansa maza uku, sun bi Shawulu wajen yaƙi. Ɗansa na fari shi ne Eliyab, na biyu shi ne Abinadab, na uku kuwa shi ne Shamma.

  20. 1 Sama’ila 17:14kusan 1063 K.H.

    Dawuda shi ne ɗan autansu. Manyan ’yan mazan nan uku suka bi Shawulu.

  21. 1 Sama’ila 17:15kusan 1063 K.H.

    Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa.

  22. 1 Sama’ila 17:16kusan 1063 K.H.

    Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.

  23. 1 Sama’ila 17:17kusan 1063 K.H.

    Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri.

  24. 1 Sama’ila 17:18kusan 1063 K.H.

    Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu.

  25. 1 Sama’ila 17:19kusan 1063 K.H.

    Suna tare da Shawulu da kuma dukan mutanen Isra’ila a Kwarin Ela, suna can suna yaƙi da Filistiyawa.”