Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 15:3kusan 1079 K.H.

    Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ”

  2. 1 Sama’ila 15:4kusan 1079 K.H.

    Sai Shawulu ya tattara sojoji, ya ƙidaya su a Telayim, ya sami su dubu ɗari biyu da dubu goma daga Yahuda.

  3. 1 Sama’ila 15:5kusan 1079 K.H.

    Shawulu ya tafi birnin Amalek ya yi kwanto a kwari.

  4. 1 Sama’ila 15:6kusan 1079 K.H.

    Sai Shawulu ya ce wa Keniyawa, “Ku tashi ku bar Amalekawa don kada in hallaka ku tare da su, saboda kun yi wa dukan Isra’ilawa kirki, lokacin da suka fito daga Masar.” Saboda haka Keniyawa suka tashi suka bar Amalekawa.

  5. 1 Sama’ila 15:7kusan 1079 K.H.

    Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar.

  6. 1 Sama’ila 15:8kusan 1079 K.H.

    Ya kama Agag sarkin Amalekawa da rai. Ya kuma hallaka dukan mutanensa da takobi.

  7. 1 Sama’ila 15:9kusan 1079 K.H.

    Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da ’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka.

  8. 1 Sama’ila 15:10kusan 1079 K.H.

    Sai Ubangiji ya yi magana da Sama’ila ya ce,

  9. 1 Sama’ila 15:11kusan 1079 K.H.

    “Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.

  10. 1 Sama’ila 15:12kusan 1079 K.H.

    Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.

  11. 1 Sama’ila 15:13kusan 1079 K.H.

    Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.”

  12. 1 Sama’ila 15:14kusan 1079 K.H.

    Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?”

  13. 1 Sama’ila 15:15kusan 1079 K.H.

    Shawulu ya amsa ya ce, “Sojoji ne suka kawo su daga Amalekawa. Sun bar tumaki da shanu masu kyau da rai don su yi wa Ubangiji Allahnka hadaya, amma sauran mun hallaka duka.”

  14. 1 Sama’ila 15:16kusan 1079 K.H.

    Sama’ila ya ce, “Dakata, bari in faɗa maka abin da Ubangiji ya ce mini jiya da dare.” Shawulu ya ce, “Gaya mini.”

  15. 1 Sama’ila 15:17kusan 1079 K.H.

    Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila.

  16. 1 Sama’ila 15:18kusan 1079 K.H.

    Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’

  17. 1 Sama’ila 15:19kusan 1079 K.H.

    Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?”

  18. 1 Sama’ila 15:20kusan 1079 K.H.

    Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu.

  19. 1 Sama’ila 15:21kusan 1079 K.H.

    Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”

  20. 1 Sama’ila 15:22kusan 1079 K.H.

    Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.

  21. 1 Sama’ila 15:23kusan 1079 K.H.

    Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”

  22. 1 Sama’ila 15:24kusan 1079 K.H.

    Sai Shawulu ya ce wa Sama’ila, “Na yi zunubi, na ƙi bin umarnin Ubangiji, na kuma ƙi bin maganarka. Na ji tsoron mutane ne shi ya sa na bi maganarsu.

  23. 1 Sama’ila 15:25kusan 1079 K.H.

    Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.”

  24. 1 Sama’ila 15:26kusan 1079 K.H.

    Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.”

  25. 1 Sama’ila 15:27kusan 1079 K.H.

    Da Sama’ila ya juya zai tafi, sai Shawulu ya kama bakin rigarsa, sai rigar ta yage.