- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 14:30kusan 1087 K.H.
Da yaya zai kasance ke nan da a ce an bar sojoji suka ci abincin da suka ƙwace daga abokan gābansu? Ai, da gawawwakin Filistiyawan da aka kashe sun fi haka.”
- 1 Sama’ila 14:31kusan 1087 K.H.
A ranan nan Isra’ilawa suka yi ta kashe Filistiyawa daga Mikmash har zuwa Aiyalon. Bayan haka gajiya ta kama su sosai saboda yunwa.
- 1 Sama’ila 14:32kusan 1087 K.H.
Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yayyanka su, suka ci naman ɗanye.
- 1 Sama’ila 14:33kusan 1087 K.H.
Sai wani mutum ya ce wa Shawulu, “Duba, ga mutane suna zunubi ga Ubangiji, suna cin nama da jini.” Shawulu ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse zuwa wurina nan da nan.”
- 1 Sama’ila 14:34kusan 1087 K.H.
Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo shanu da tumaki a nan, su yayyanka, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Haka nan kowa ya kawo saniyarsa a daren, ya yanka a can.
- 1 Sama’ila 14:35kusan 1087 K.H.
Sa’an nan Shawulu ya gina wa Ubangiji bagade. Wannan ne bagade na farkon da ya gina.
- 1 Sama’ila 14:36kusan 1087 K.H.
Shawulu ya ce, “Mu bi gangara mu fafare Filistiyawa da dare mu washe su har gari yă waye, mu kuma karkashe kowannensu, kada mu bar wani da rai.” Suka ce, “Ka yi duk abin da ka ga ya fi maka kyau.” Amma firist ya ce, “Bari mu nemi nufin Allah tukuna.”
- 1 Sama’ila 14:37kusan 1087 K.H.
Saboda haka Shawulu ya tambayi Allah ya ce, “Mu bi bayan Filistiyawa? Za ka bashe su a hannun Isra’ila?” Amma Allah bai ba shi amsa a ranar ba.
- 1 Sama’ila 14:38kusan 1087 K.H.
Saboda haka Shawulu ya ce, “Ku zo nan dukanku shugabannin rundunoni, mu bincika mu san zunubin da ya kawo rashin amsan nan yau.
- 1 Sama’ila 14:39kusan 1087 K.H.
Muddin Ubangiji wanda ya ceci Isra’ila yana raye, ko da ɗana Yonatan ne ya yi zunubin, dole yă mutu.” Amma ba ko ɗaya daga cikinsu da ya ce uffam.
- 1 Sama’ila 14:40kusan 1087 K.H.
Sai Shawulu ya ce wa dukan Isra’ilawa, “Ku tsaya a can, ni kuma da Yonatan ɗana mu tsaya a nan.” Mutanen suka ce, “Ka yi abin da ya fi maka kyau.”
- 1 Sama’ila 14:41kusan 1087 K.H.
Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, “Me ya sa ba ka amsa mini addu’ata a yau ba? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Yonatan, ka nuna mana ta wurin Urim, amma idan laifin mutanen ne ka amsa ta wurin Tummim.” Ba a sami mutane da laifi ba, amma ƙuri’a ta fāɗa a kan Yonatan da Shawulu.
- 1 Sama’ila 14:42kusan 1087 K.H.
Shawulu ya ce, “Ku jefa ƙuri’a tsakanina da ɗana Yonatan.” Sai ƙuri’ar ta fāɗa a kan Yonatan.
- 1 Sama’ila 14:43kusan 1087 K.H.
Sai Shawulu ya ce wa Yonatan, “Gaya mini mene ne ka yi.” Yonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana zuma kaɗan daga gindin sandanta. Yanzu kuwa dole in mutu!”
- 1 Sama’ila 14:44kusan 1087 K.H.
Shawulu ya ce, “Bari hukunci mai tsanani na Allah yă kasance a kaina, in ba ka mutu ba, Yonatan.”
- 1 Sama’ila 14:45kusan 1087 K.H.
Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin Ubangiji yana raye, ko gashin kansa ɗaya ba zai fāɗi a ƙasa ba, gama abin da ya yi yau, Allah ne yana tare da shi.” Ta haka mutane suka ceci Yonatan daga mutuwa.
- 1 Sama’ila 14:46kusan 1087 K.H.
Sai Shawulu ya daina bin Filistiyawa, suka koma ƙasarsu.
- 1 Sama’ila 14:47kusan 1087 K.H.
Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.
- 1 Sama’ila 14:48kusan 1087 K.H.
Ya yi jaruntaka sosai, ya ci Amalekawa da yaƙi, ya kuma ceci Isra’ila daga hannuwan waɗanda suka ƙwace musu kaya.
- 1 Sama’ila 14:49kusan 1087 K.H.
’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban ’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal.
- 1 Sama’ila 14:50kusan 1087 K.H.
Sunan matarsa kuwa Ahinowam, ’yar Ahimawaz. Sunan shugaban ƙungiyar sojan Shawulu kuwa Abner ne ɗan Ner, shi Ner kuwa ɗan’uwan mahaifin Shawulu ne.
- 1 Sama’ila 14:51kusan 1087 K.H.
Mahaifin Shawulu, Kish da kuma Ner mahaifin Abner, ’ya’yan Abiyel ne.
- 1 Sama’ila 14:52kusan 1087 K.H.
Dukan kwanakin Shawulu sun kasance na yaƙe-yaƙe da Filistiyawa ne. Duk lokacin da Shawulu ya ga ƙaƙƙarfan mutum ko jarumi, sai yă ɗauke shi aikin sojansa.
- 1 Sama’ila 15:1kusan 1079 K.H.
Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ni ne wanda Ubangiji ya aika in shafe ka ka zama sarki bisa mutanensa Isra’ila. Saurara yanzu ka ji saƙo daga wurin Ubangiji.
- 1 Sama’ila 15:2kusan 1079 K.H.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan hori Amalekawa saboda abin da suka yi wa Isra’ila sa’ad da suka ba su wahala yayinda suka fito daga Masar.