Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 13:3kusan 1093 K.H.

    Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!”

  2. 1 Sama’ila 13:4kusan 1093 K.H.

    Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal.

  3. 1 Sama’ila 13:5kusan 1093 K.H.

    Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can.

  4. 1 Sama’ila 13:6kusan 1093 K.H.

    Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi.

  5. 1 Sama’ila 13:7kusan 1093 K.H.

    Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Shawulu ya zauna Gilgal, dukan ƙungiyoyi sojojin da suke tare da shi suka yi rawan jiki don tsoro.

  6. 1 Sama’ila 13:8kusan 1093 K.H.

    Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa.

  7. 1 Sama’ila 13:9kusan 1093 K.H.

    Sai ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.” Sai Shawulu ya miƙa hadaya ta ƙonawa.

  8. 1 Sama’ila 13:10kusan 1093 K.H.

    Daidai yana gama miƙa hadaya ke nan sai Sama’ila ya iso. Shawulu kuma ya fito domin yă yi masa maraba.

  9. 1 Sama’ila 13:11kusan 1093 K.H.

    Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash,

  10. 1 Sama’ila 13:12kusan 1093 K.H.

    sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.”

  11. 1 Sama’ila 13:13kusan 1093 K.H.

    Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada.

  12. 1 Sama’ila 13:14kusan 1093 K.H.

    Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”

  13. 1 Sama’ila 13:15kusan 1093 K.H.

    Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.

  14. 1 Sama’ila 13:16kusan 1093 K.H.

    Shawulu da ɗansa Yonatan da mutanen da suke tare da shi suka zauna a Geba ta Benyamin. Sa’an nan Filistiyawa suka yi sansani a Mikmash.

  15. 1 Sama’ila 13:17kusan 1093 K.H.

    Rundunar mayaƙa uku suka fito daga sansani Filistiyawa. Ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.

  16. 1 Sama’ila 13:18kusan 1093 K.H.

    Runduna guda kuma ta nufi Bet-Horon, ɗayan kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar Kwarin Ziboyim wajen jeji.

  17. 1 Sama’ila 13:19kusan 1093 K.H.

    Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.”

  18. 1 Sama’ila 13:20kusan 1093 K.H.

    Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu.

  19. 1 Sama’ila 13:21kusan 1093 K.H.

    Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.

  20. 1 Sama’ila 13:22kusan 1093 K.H.

    A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai.

  21. 1 Sama’ila 13:23kusan 1093 K.H.

    Ana nan sai sojojin Filistiyawa suka fita zuwa mashigin Mikmash.

  22. 1 Sama’ila 14:1kusan 1087 K.H.

    Wata rana Yonatan ɗan Shawulu ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo mu tafi wajen sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai gaya wa mahaifinsa ba.

  23. 1 Sama’ila 14:2kusan 1087 K.H.

    Shawulu kuwa na zaune a gindin itacen rumman a bayan garin Gibeya a Migron. Tare da shi akwai mutum wajen ɗari shida.

  24. 1 Sama’ila 14:3kusan 1087 K.H.

    A cikinsu akwai Ahiya sanye da efod. Shi yaron Ikabod ɗan’uwan Ahitub ne, ɗan Finehas, ɗan Eli, firist na Ubangiji a Shilo. Ba wanda ya san cewa Yonatan ya tafi wani wuri.

  25. 1 Sama’ila 14:4kusan 1087 K.H.

    A kowane gefe na mashigin da Yonatan ya so yă bi zuwa wurin Filistiyawa, akwai hawa mai tsawo, ana kira ɗaya Bozez, ɗayan kuma ana kira Senet.