- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 10:20kusan 1095 K.H.
Sa’ad da Sama’ila ya kawo dukan Isra’ila gaba, kabila-kabila, sai aka zaɓi kabilar Benyamin ta wurin jefa ƙuri’a.
- 1 Sama’ila 10:21kusan 1095 K.H.
Sai ya kawo kabilar Benyamin gaba, iyali-iyali, aka zaɓi iyalin Matri. A ƙarshe aka zaɓi Shawulu ɗan Kish. Amma da aka neme shi sai ba a same shi ba.
- 1 Sama’ila 10:22kusan 1095 K.H.
Suka ƙara nemi bayani daga Ubangiji suka ce, “Mutumin ya zo nan kuwa?” Ubangiji ya ce, “I, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”
- 1 Sama’ila 10:23kusan 1095 K.H.
Suka ruga suka kawo shi. Da ya tsaya cikin mutane, sai ya fi kowa tsayi.
- 1 Sama’ila 10:24kusan 1095 K.H.
Sama’ila ya ce wa dukan mutane, “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa ko? Ba wani kamar sa a cikin dukan mutane.” Sai mutane suka tā da murya suka ce, “Ran sarki yă daɗe.”
- 1 Sama’ila 10:25kusan 1095 K.H.
Sama’ila kuwa ya bayyana wa mutane ƙa’idodin sarauta. Ya rubuta su cikin littafi ya ajiye a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya sallame mutane, kowa ya koma gidansa.
- 1 Sama’ila 10:26kusan 1095 K.H.
Shawulu ma ya tafi gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawan da Allah ya taɓa zuciyarsu.
- 1 Sama’ila 10:27kusan 1095 K.H.
Amma waɗansu ’yan iska suka ce, “Yaya wannan mutum zai iya cetonmu?” Suka rena shi suka ƙi su kawo masa kyautai. Amma Shawulu bai ce uffam ba.
- 1 Sama’ila 11:1kusan 1095 K.H.
Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”
- 1 Sama’ila 11:2kusan 1095 K.H.
Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.”
- 1 Sama’ila 11:3kusan 1095 K.H.
Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”
- 1 Sama’ila 11:4kusan 1095 K.H.
Da manzannin suka zo Gibeya garin Shawulu, suka gaya wa mutane wannan sharaɗin, suka yi kuka mai zafi.
- 1 Sama’ila 11:5kusan 1095 K.H.
A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu.
- 1 Sama’ila 11:6kusan 1095 K.H.
Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.
- 1 Sama’ila 11:7kusan 1095 K.H.
Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.
- 1 Sama’ila 11:8kusan 1095 K.H.
Mutanen Isra’ila sun kai dubu ɗari uku. Mutanen Yahuda kuma dubu talatin, sa’ad da Shawulu ya tara su a Bezek.
- 1 Sama’ila 11:9kusan 1095 K.H.
Suka ce wa ’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da ’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki.
- 1 Sama’ila 11:10kusan 1095 K.H.
Suka ce wa Ammonawa, “Gobe za mu miƙa wuya gare ku, ku kuma yi duk abin da kuka ga dama.”
- 1 Sama’ila 11:11kusan 1095 K.H.
Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.
- 1 Sama’ila 11:12kusan 1095 K.H.
Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.”
- 1 Sama’ila 11:13kusan 1095 K.H.
Shawulu ya ce, “Ba wanda zai mutu yau, gama Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana.”
- 1 Sama’ila 11:14kusan 1095 K.H.
Sai Sama’ila ya ce wa mutane, “Ku zo mu tafi Gilgal, a can za a yi wankan sarauta.”
- 1 Sama’ila 11:15kusan 1095 K.H.
Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.
- 1 Sama’ila 12:1kusan 1095 K.H.
Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki.
- 1 Sama’ila 12:2kusan 1095 K.H.
Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro.