Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 8:19kusan 1112 K.H.

    Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”

  2. 1 Sama’ila 8:20kusan 1112 K.H.

    Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.

  3. 1 Sama’ila 8:21kusan 1112 K.H.

    Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.

  4. 1 Sama’ila 8:22kusan 1112 K.H.

    Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”

  5. 1 Sama’ila 9:1kusan 1095 K.H.

    An yi wani mutum, attajiri daga kabilar Benyamin, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror na iyalin Bekorat daga dangin Afiya.

  6. 1 Sama’ila 9:2kusan 1095 K.H.

    Yana da ɗa mai suna Shawulu, wani kyakkyawan saurayi. A cikin mutanen Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya kuma fi kowa tsaye.

  7. 1 Sama’ila 9:3kusan 1095 K.H.

    To, ana nan sai jakunan Kish mahaifin Shawulu suka ɓace. Kish ya ce wa ɗansa, “Tashi ka tafi tare da wani daga cikin bayi, ku nemo jakunan.”

  8. 1 Sama’ila 9:4kusan 1095 K.H.

    Suka bi ta ƙasar tudu ta Efraim, suka ratsa ta ƙasar Shalisha amma ba su same su ba. Suka bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba sai suka bi ta ƙasar Benyamin, a can ma ba su same su ba.

  9. 1 Sama’ila 9:5kusan 1095 K.H.

    Da suka iso gunduman Zuf, sai Shawulu ya ce wa bawan da yake tare da shi, “Zo mu koma kada mahaifina yă bar damuwa a kan jakuna, yă shiga damuwa game da mu.”

  10. 1 Sama’ila 9:6kusan 1095 K.H.

    Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.”

  11. 1 Sama’ila 9:7kusan 1095 K.H.

    Shawulu ya ce wa bawan, “Idan muka isa can, me za mu ba wa mutumin? Ga shi abinci guzurinmu duk ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu kai wa mutumin Allahn nan. Me muke da shi?”

  12. 1 Sama’ila 9:8kusan 1095 K.H.

    Bawan ya sāke ce masa, “Duba ina da kwatar azurfar da zan ba wa mutumin Allah don yă gaya mana wace hanya ce za mu bi.”

  13. 1 Sama’ila 9:9kusan 1095 K.H.

    (A dā a Isra’ila, in wani yana so yă nemi nufin Allah, mutumin yakan ce, “Zo mu tafi wajen mai duba.” Gama wanda ake ce da shi annabi a yanzu, a dā ana kiransa mai duba ne.)

  14. 1 Sama’ila 9:10kusan 1095 K.H.

    Shawulu ya ce wa bawansa, “Madalla, zo mu tafi.” Sai suka kama hanya suka nufi birnin da mutumin Allah yake.

  15. 1 Sama’ila 9:11kusan 1095 K.H.

    Sa’ad da suke haura tudun zuwa birnin, sai suka sadu da waɗansu ’yan mata sun fito za su ɗiban ruwa. Sai suka tambaye su, suka ce, “Mai duba yana nan?”

  16. 1 Sama’ila 9:12kusan 1095 K.H.

    ’Yan matan suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu.

  17. 1 Sama’ila 9:13kusan 1095 K.H.

    Da zarar kun shiga garin, za ku same shi kafin yă tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu. Gama jama’a ba za su ci ba, sai ya kai can ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura da sauri, za ku same.”

  18. 1 Sama’ila 9:14kusan 1095 K.H.

    Suka haura zuwa birnin, da shigarsu sai ga Sama’ila ya nufo su a hanyarsa ta zuwa kan tudu.

  19. 1 Sama’ila 9:15kusan 1095 K.H.

    Kafin zuwa Shawulu, Ubangiji ya riga ya bayyana wa Sama’ila ya ce,

  20. 1 Sama’ila 9:16kusan 1095 K.H.

    “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”

  21. 1 Sama’ila 9:17kusan 1095 K.H.

    Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”

  22. 1 Sama’ila 9:18kusan 1095 K.H.

    Shawulu ya sami Sama’ila a hanyar shiga gari, sai ya tambaye shi ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini gidan mai duba?”

  23. 1 Sama’ila 9:19kusan 1095 K.H.

    Sama’ila ya ce, “Ni ne mai duban, ka yi gaba zuwa ka tudu, gama yau za ka ci tare da ni, da safe kuma in sallame ka, in gaya muku duk abin da yake a zuciyarku.

  24. 1 Sama’ila 9:20kusan 1095 K.H.

    Game da jakunan da suka ɓace kwana uku kuwa, kada ka damu, an same su. Ga wane ne Isra’ila ta sa dukan zuciya, in ba ga kai da kuma dukan iyalin mahaifinka ba?”

  25. 1 Sama’ila 9:21kusan 1095 K.H.

    Shawulu ya ce, “Ashe, ni ba mutumin Benyamin ba ne daga ƙaramar kabila ta Isra’ila? Dangina kuma ba shi ba ne mafi kakanni a cikin kabilar Benyamin ba? Yaya za ka faɗa mini irin wannan magana.”