Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 7:11kusan 1120 K.H.

    Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.

  2. 1 Sama’ila 7:12kusan 1120 K.H.

    Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”

  3. 1 Sama’ila 7:13kusan 1120 K.H.

    Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.

  4. 1 Sama’ila 7:14kusan 1120 K.H.

    Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa.

  5. 1 Sama’ila 7:15kusan 1131 K.H.

    Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa.

  6. 1 Sama’ila 7:16kusan 1131 K.H.

    Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a.

  7. 1 Sama’ila 7:17kusan 1131 K.H.

    Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.

  8. 1 Sama’ila 8:1kusan 1112 K.H.

    Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

  9. 1 Sama’ila 8:2kusan 1112 K.H.

    Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.

  10. 1 Sama’ila 8:3kusan 1112 K.H.

    Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.

  11. 1 Sama’ila 8:4kusan 1112 K.H.

    Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.

  12. 1 Sama’ila 8:5kusan 1112 K.H.

    Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”

  13. 1 Sama’ila 8:6kusan 1112 K.H.

    Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.

  14. 1 Sama’ila 8:7kusan 1112 K.H.

    Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.

  15. 1 Sama’ila 8:8kusan 1112 K.H.

    Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.

  16. 1 Sama’ila 8:9kusan 1112 K.H.

    Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”

  17. 1 Sama’ila 8:10kusan 1112 K.H.

    Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

  18. 1 Sama’ila 8:11kusan 1112 K.H.

    Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.

  19. 1 Sama’ila 8:12kusan 1112 K.H.

    Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.

  20. 1 Sama’ila 8:13kusan 1112 K.H.

    Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.

  21. 1 Sama’ila 8:14kusan 1112 K.H.

    Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.

  22. 1 Sama’ila 8:15kusan 1112 K.H.

    Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.

  23. 1 Sama’ila 8:16kusan 1112 K.H.

    Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.

  24. 1 Sama’ila 8:17kusan 1112 K.H.

    Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.

  25. 1 Sama’ila 8:18kusan 1112 K.H.

    Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”