- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 9:22kusan 1095 K.H.
Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin.
- 1 Sama’ila 9:23kusan 1095 K.H.
Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.”
- 1 Sama’ila 9:24kusan 1095 K.H.
Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.
- 1 Sama’ila 9:25kusan 1095 K.H.
Bayan suka gangaro daga tudu zuwa cikin gari, Sai Sama’ila ya yi magana da Shawulu a ɗakin samansa.
- 1 Sama’ila 9:26kusan 1095 K.H.
Da asuba sai suka tashi, Sama’ila ya kira Shawulu daga ɗakin sama ya ce, “Ka shirya, zan sallame ka.” Da Shawulu ya shirya, sai Sama’ila da Shawulu suka fita waje tare.
- 1 Sama’ila 9:27kusan 1095 K.H.
Suna dab da ƙarshen gari, sai Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ka ce wa bawanka yă yi gaba, kai ka ɗan dakata a nan tukuna, domin in ba ka saƙo daga Allah.”
- 1 Sama’ila 10:1kusan 1095 K.H.
Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.
- 1 Sama’ila 10:2kusan 1095 K.H.
Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’
- 1 Sama’ila 10:3kusan 1095 K.H.
“Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
- 1 Sama’ila 10:4kusan 1095 K.H.
Za su gaishe ka, su ba ka burodi biyu, kai kuwa sai ka karɓa.
- 1 Sama’ila 10:5kusan 1095 K.H.
“Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci.
- 1 Sama’ila 10:6kusan 1095 K.H.
Ruhun Ubangiji zai sauko a kanka da iko, za ka kuma yi annabci tare da su. Za a canja ka ka zama dabam.
- 1 Sama’ila 10:7kusan 1095 K.H.
Da zarar waɗannan alamu sun cika, sai ka aikata duk abin da kana iya yi gama Allah yana tare da kai.
- 1 Sama’ila 10:8kusan 1095 K.H.
“Ka sha gabana zuwa Gilgal. Lalle zan gangara wurinka domin in miƙa hadaya ta ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai sai na zo wurinka na kuma gaya maka abin da za ka yi.”
- 1 Sama’ila 10:9kusan 1095 K.H.
Da Shawulu ya juya zai bar Sama’ila, sai Allah ya canja wa Shawulu zuciya, alamun nan kuwa suka cika a ranar.
- 1 Sama’ila 10:10kusan 1095 K.H.
Da suka iso Gibeya, jerin gwanon annabawa suka sadu da shi Ruhun Allah kuma ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga yin annabci tare da su.
- 1 Sama’ila 10:11kusan 1095 K.H.
Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi a dā suka gan shi yana annabci tare da annabawa, sai suka tambayi juna, suka ce, “Me ya faru da ɗan Kish? Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”
- 1 Sama’ila 10:12kusan 1095 K.H.
Wani mutumin da yake zama a can ya ce, “Wane ne kuma mahaifinsu?” Ta haka sai wannan ya zama karin magana cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa?”
- 1 Sama’ila 10:13kusan 1095 K.H.
Bayan da Shawulu ya gama annabci sai ya haura ya tafi tudu.
- 1 Sama’ila 10:14kusan 1095 K.H.
Sai ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya tambaye shi da baransa ya ce, “Ina kuka je?” Shawulu ya ce, “Mun tafi neman jakuna, amma da ba mu same su ba sai muka tafi wurin Sama’ila.”
- 1 Sama’ila 10:15kusan 1095 K.H.
Ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya ce, “Faɗa mini abin da Sama’ila ya ce maka.”
- 1 Sama’ila 10:16kusan 1095 K.H.
Shawulu ya ce, “Ya tabbatar mana cewa an riga an sami jakuna.” Amma bai gaya wa ɗan’uwan mahaifinsa abin da Sama’ila ya ce game da sarauta ba.
- 1 Sama’ila 10:17kusan 1095 K.H.
Sama’ila ta tattara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa
- 1 Sama’ila 10:18kusan 1095 K.H.
ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na fito da Isra’ila daga Masar, na kuma cece ku daga hannun Masarawa da dukan mulkokin da suka wahalshe ku.’
- 1 Sama’ila 10:19kusan 1095 K.H.
Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.”