- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 4:16kusan 1141 K.H.
Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”
- 1 Sama’ila 4:17kusan 1141 K.H.
Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
- 1 Sama’ila 4:18kusan 1141 K.H.
Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
- 1 Sama’ila 4:19kusan 1141 K.H.
Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.
- 1 Sama’ila 4:20kusan 1141 K.H.
Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.
- 1 Sama’ila 4:21kusan 1141 K.H.
Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.
- 1 Sama’ila 4:22kusan 1141 K.H.
Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
- 1 Sama’ila 5:1kusan 1141 K.H.
Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod.
- 1 Sama’ila 5:2kusan 1141 K.H.
Sa’an nan suka ɗauki akwatin alkawarin suka kai shi cikin haikalin gunkinsu Dagon, suka ajiye kusa da Dagon.
- 1 Sama’ila 5:3kusan 1141 K.H.
Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.
- 1 Sama’ila 5:4kusan 1141 K.H.
Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.
- 1 Sama’ila 5:5kusan 1141 K.H.
Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau.
- 1 Sama’ila 5:6kusan 1141 K.H.
Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai.
- 1 Sama’ila 5:7kusan 1141 K.H.
Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.”
- 1 Sama’ila 5:8kusan 1141 K.H.
Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.
- 1 Sama’ila 5:9kusan 1141 K.H.
Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro.
- 1 Sama’ila 5:10kusan 1141 K.H.
Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, “An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin yă kashe mu da mutanenmu.”
- 1 Sama’ila 5:11kusan 1141 K.H.
Saboda haka suka kira ga dukan shugabannin Filistiyawa suka ce, “Ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila inda ya fito; in ba haka ba zai kashe mu da mutanenmu.” Gama mutuwa ta cika garin da tsoro. Hannun Allah ya yi nauyi a kansa.
- 1 Sama’ila 5:12kusan 1141 K.H.
Waɗanda ba su mutu ba kuwa, sun kamu da marurai. Kukan birnin kuwa ta hau har zuwa sama.
- 1 Sama’ila 6:1kusan 1140 K.H.
Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.
- 1 Sama’ila 6:2kusan 1140 K.H.
Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito.”
- 1 Sama’ila 6:3kusan 1140 K.H.
Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba.
- 1 Sama’ila 6:4kusan 1140 K.H.
Filistiyawa suka ce, “Wace irin hadaya don laifi za mu aika masa?” Suka ce, “Marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa. Saboda annoba iri ɗaya ce ta buga ku da shugabanninku.
- 1 Sama’ila 6:5kusan 1140 K.H.
Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye da suke hallaka gari, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila. Wataƙila zai ɗauke hukuncinsa daga gare ku da allolinku da kuma ƙasarku.
- 1 Sama’ila 6:6kusan 1140 K.H.
Me ya sa kun taurare kanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka yi? Da ya ba su matsanancin wahala, ba su bar Isra’ilawa suka tafi hanyarsu ba?