- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 3:12kusan 1165 K.H.
A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.
- 1 Sama’ila 3:13kusan 1165 K.H.
Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi; ’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.
- 1 Sama’ila 3:14kusan 1165 K.H.
Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’ ”
- 1 Sama’ila 3:15kusan 1165 K.H.
Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,
- 1 Sama’ila 3:16kusan 1165 K.H.
amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.”
- 1 Sama’ila 3:17kusan 1165 K.H.
Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka.
- 1 Sama’ila 3:18kusan 1165 K.H.
Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.”
- 1 Sama’ila 3:19kusan 1165 K.H.
Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba.
- 1 Sama’ila 3:20kusan 1165 K.H.
Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji.
- 1 Sama’ila 3:21kusan 1165 K.H.
Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa.
- 1 Sama’ila 4:1kusan 1141 K.H.
Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi. Isra’ilawa suka fita yaƙi da Filistiyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a Ebenezer, Filistiyawa kuma a Afek.
- 1 Sama’ila 4:2kusan 1141 K.H.
Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā.
- 1 Sama’ila 4:3kusan 1141 K.H.
Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.”
- 1 Sama’ila 4:4kusan 1141 K.H.
Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.
- 1 Sama’ila 4:5kusan 1141 K.H.
Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga.
- 1 Sama’ila 4:6kusan 1141 K.H.
Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?” Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin,
- 1 Sama’ila 4:7kusan 1141 K.H.
sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, “Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba.
- 1 Sama’ila 4:8kusan 1141 K.H.
Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji.
- 1 Sama’ila 4:9kusan 1141 K.H.
Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi.”
- 1 Sama’ila 4:10kusan 1141 K.H.
Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin.
- 1 Sama’ila 4:11kusan 1141 K.H.
Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.
- 1 Sama’ila 4:12kusan 1141 K.H.
A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa.
- 1 Sama’ila 4:13kusan 1141 K.H.
Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.
- 1 Sama’ila 4:14kusan 1141 K.H.
Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu? Mutumin ya rugo wurin Eli,
- 1 Sama’ila 4:15kusan 1141 K.H.
wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.