Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 2:23kusan 1165 K.H.

    Saboda haka ya ce musu, “Don me kuke yin waɗannan abubuwa? Na sami labari daga wurin mutane a kan duk ayyukan muguntanku.

  2. 1 Sama’ila 2:24kusan 1165 K.H.

    A’a, ’ya’yana ba labari mai kyau nake ji cikin mutanen Ubangiji ba.

  3. 1 Sama’ila 2:25kusan 1165 K.H.

    In mutum ya yi wa wani laifi Allah yakan kāre shi; amma in mutum ya yi wa Ubangiji zunubi wa zai kāre shi?” Duk da haka, ’ya’yansa ba su kula da gargaɗin mahaifinsu ba, domin nufin Ubangiji ne yă hallaka su.

  4. 1 Sama’ila 2:26kusan 1165 K.H.

    Yaron nan Sama’ila ya dinga girma cikin kwarjini da cikin tagomashi a gaba Ubangiji da mutane.

  5. 1 Sama’ila 2:27kusan 1165 K.H.

    Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?

  6. 1 Sama’ila 2:28kusan 1165 K.H.

    Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.

  7. 1 Sama’ila 2:29kusan 1165 K.H.

    Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’

  8. 1 Sama’ila 2:30kusan 1165 K.H.

    “Saboda haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na yi alkawari cewa gidanka da gidan mahaifinka za su yi mini hidima a gabana har abada.’ Amma, yanzu Allah ya ce, ba zai yiwu ba; waɗanda suke girmama ni; Ni ma zan girmama su. Amma waɗanda suke ƙasƙantar da ni, haka za a ƙasƙantar da su.

  9. 1 Sama’ila 2:31kusan 1165 K.H.

    Lokaci yana zuwa sa’ad da zan rage ƙarfinka da ƙarfin iyalin gidan mahaifinka. Domin kada a sāke samun tsohon mutum a zuriyarka.

  10. 1 Sama’ila 2:32kusan 1165 K.H.

    Za ka zama da ɓacin rai a mazaunina ko da yake za a yi wa Isra’ila alheri. A zuriyarka ba za a taɓa samun tsohon mutum ba.

  11. 1 Sama’ila 2:33kusan 1165 K.H.

    Kowannenku da ban kashe daga hidima a bagadena ba, za a bar shi don yă cika idanunka da hawaye da kuma baƙin ciki, dukan sauran zuriyarka kuwa za su mutu a ƙuruciyarsu.

  12. 1 Sama’ila 2:34kusan 1165 K.H.

    “ ‘Abin da kuma ya faru da ’ya’yanka biyu Hofni da Finehas zai zama alama a gare ka; saboda mutuwarsu za tă zama a rana ɗaya.

  13. 1 Sama’ila 2:35kusan 1165 K.H.

    Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.

  14. 1 Sama’ila 2:36kusan 1165 K.H.

    Sa’an nan duk wanda ya rage a zuriyarka zai zo yă durƙusa a gabansa yă roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa yă taimaki firistoci da aiki domin yă sami abin da zai ci.’ ”

  15. 1 Sama’ila 3:1kusan 1165 K.H.

    Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.

  16. 1 Sama’ila 3:2kusan 1165 K.H.

    Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.

  17. 1 Sama’ila 3:3kusan 1165 K.H.

    Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.

  18. 1 Sama’ila 3:4kusan 1165 K.H.

    Sai Ubangiji ya kira Sama’ila. Sama’ila ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  19. 1 Sama’ila 3:5kusan 1165 K.H.

    Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Eli ya ce, “Ɗana ban kira ba, je ka kwanta”. Saboda haka ya tafi ya kwanta.

  20. 1 Sama’ila 3:6kusan 1165 K.H.

    Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”

  21. 1 Sama’ila 3:7kusan 1165 K.H.

    Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.

  22. 1 Sama’ila 3:8kusan 1165 K.H.

    Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sai Eli ya gane cewa Ubangiji ne ke kira yaron.

  23. 1 Sama’ila 3:9kusan 1165 K.H.

    Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.

  24. 1 Sama’ila 3:10kusan 1165 K.H.

    Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”

  25. 1 Sama’ila 3:11kusan 1165 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.