- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1050–1010 BC
Samuel & King Saul
Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sama’ila 15:28kusan 1079 K.H.
Sama’ila ya ce masa, “Ubangiji ya yage masarautar Isra’ila daga gare ka yau, ya ba wa wani daga cikin maƙwabtanka wanda ya fi ka.
- 1 Sama’ila 15:29kusan 1079 K.H.
Shi wanda yake Ɗaukakar Isra’ila ba ya ƙarya ko yă canja zuciyarsa, gama shi ba mutum ba ne da zai canja zuciyarsa.”
- 1 Sama’ila 15:30kusan 1079 K.H.
Shawulu ya ce, “Na yi zunubi. Amma ina roƙonka ka ba ni girma a gaban dattawan mutanena da kuma a gaban Isra’ila, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji Allahnka sujada.”
- 1 Sama’ila 15:31kusan 1079 K.H.
Saboda haka sai Sama’ila ya koma tare da Shawulu, Shawulu kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
- 1 Sama’ila 15:32kusan 1079 K.H.
Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Kawo mini Agag sarkin Amalekawa.” Agag kuwa ya zo wurinsa daure da sarƙa, yana tunani cewa, “Tabbatacce zancen mutuwa dai ya wuce.”
- 1 Sama’ila 15:33kusan 1079 K.H.
Amma Sama’ila ya ce, “Yadda takobinka ya sa mata suka rasa ’ya’ya, haka mahaifiyarka za tă zama marar ’ya’ya a cikin mata.” Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji.
- 1 Sama’ila 15:34kusan 1079 K.H.
Sai Sama’ila ya tafi Rama, amma Shawulu ya haura zuwa gidansa a Gibeya na Shawulu.
- 1 Sama’ila 15:35kusan 1079 K.H.
Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.
- 1 Sama’ila 16:1kusan 1063 K.H.
Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta makoki saboda Shawulu? Na riga na ƙi shi da zaman sarkin Isra’ila. Ka cika ƙahonka da mai, zan aike ka zuwa wurin Yesse na Betlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza yă zama sarki.”
- 1 Sama’ila 16:2kusan 1063 K.H.
Amma Sama’ila ya ce, “Yaya zan yi haka? Ai, in Shawulu ya ji labari, zai kashe ni.” Ubangiji ya ce, “To, sai ka tafi tare da ’yar karsana ka ce, ‘Na zo don in yi wa Ubangiji hadaya.’
- 1 Sama’ila 16:3kusan 1063 K.H.
Ka gayyato Yesse a wurin hadayar, ni kuma zan gaya maka abin da za ka yi. Za ka shafe mini wanda na nuna maka.”
- 1 Sama’ila 16:4kusan 1063 K.H.
Sama’ila kuwa ya yi abin da Ubangiji ya umarce shi. Da ya isa Betlehem, sai dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Mai duba, wannan ziyara lafiya dai ko?”
- 1 Sama’ila 16:5kusan 1063 K.H.
Sama’ila ya ce, “I, lafiya ƙalau. Na zo ne domin in yi wa Ubangiji hadaya. Ku tsarkake kanku sa’an nan ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da ’ya’yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar.
- 1 Sama’ila 16:6kusan 1063 K.H.
Da isarsu, Sama’ila ya ga Eliyab sai ya yi tsammani shi ne, sai ya ce, “Lalle ga shafaffe na Ubangiji tsaye a gaban Ubangiji.”
- 1 Sama’ila 16:7kusan 1063 K.H.
Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
- 1 Sama’ila 16:8kusan 1063 K.H.
Sai Yesse ya kira Abinadab yă zo gaban Sama’ila. Amma Sama’ila ya ce, “Ko wannan ma Ubangiji bai zaɓe shi ba.”
- 1 Sama’ila 16:9kusan 1063 K.H.
Sai Yesse ya sa Shamma yă zo gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ma ba.”
- 1 Sama’ila 16:10kusan 1063 K.H.
Yesse ya sa ’ya’yansa maza bakwai suka wuce gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce masa, “Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.”
- 1 Sama’ila 16:11kusan 1063 K.H.
Don haka ya tambayi Yesse ya ce, “Su ke nan ’ya’yan maza da kake da su?” Yesse ya ce, “Har yanzu akwai ɗan autan, amma yana kiwon tumaki.” Sama’ila ya ce, “Ka aika yă zo, ba za mu zauna ba sai ya iso.”
- 1 Sama’ila 16:12kusan 1063 K.H.
Sai ya aika aka kawo shi. Ga shi kuwa kyakkyawan saurayi ne mai kyan gani. Ubangiji ya ce, “Tashi ka shafe shi, shi ne wannan.”
- 1 Sama’ila 16:13kusan 1063 K.H.
Saboda haka Sama’ila ya ɗauko ƙahon nan da yake da mai ya shafe Dawuda a gaban ’yan’uwansa. Daga wannan rana kuwa ruhun Ubangiji ya sauko wa Dawuda da iko. Sai Sama’ila ya koma Rama.
- 1 Sama’ila 16:14kusan 1063 K.H.
To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.
- 1 Sama’ila 16:15kusan 1063 K.H.
Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala.
- 1 Sama’ila 16:16kusan 1063 K.H.
Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”
- 1 Sama’ila 16:17kusan 1063 K.H.
Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.”