Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 17:45kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  2. 1 Sama’ila 17:46kusan 1063 K.H.

    Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.

  3. 1 Sama’ila 17:47kusan 1063 K.H.

    Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”

  4. 1 Sama’ila 17:48kusan 1063 K.H.

    Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.

  5. 1 Sama’ila 17:49kusan 1063 K.H.

    Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.

  6. 1 Sama’ila 17:50kusan 1063 K.H.

    Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

  7. 1 Sama’ila 17:51kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.

  8. 1 Sama’ila 17:52kusan 1063 K.H.

    Mutanen Isra’ila da na Yahuda suka rugo gaba da babbar murya, suka fafari Filistiyawa har zuwa mashigin Gat da kuma ƙofofin Ekron. Gawawwakin Filistiyawa suka bazu a hanyar Sha’arayim zuwa Gat da kuma Ekron.

  9. 1 Sama’ila 17:53kusan 1063 K.H.

    Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa.

  10. 1 Sama’ila 17:54kusan 1063 K.H.

    Dawuda ya ɗauki kan Bafilistin zuwa Urushalima. Sai Dawuda ya ajiye kayan yaƙin Bafilistin a tentinsa.

  11. 1 Sama’ila 17:55kusan 1063 K.H.

    Yayinda Shawulu yake kallon Dawuda sa’ad da za shi yă yaƙi Bafilistin, sai ya tambayi Abner, komandan rundunarsa ya ce, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya ce ran sarki yă daɗe, “Ban sani ba.”

  12. 1 Sama’ila 17:56kusan 1063 K.H.

    Sarki ya ce, “Ka tambaya mini ko yaron wane ne wannan saurayi.”

  13. 1 Sama’ila 17:57kusan 1063 K.H.

    Dawuda yana dawowa daga karkashe Filistiyawa ke nan, sai Abner ya kai shi gaban Shawulu, riƙe da kan Bafilistin.

  14. 1 Sama’ila 17:58kusan 1063 K.H.

    Sai Shawulu ya ce, “Kai ɗan wane ne, saurayi?” Dawuda ya ce, “Ni ɗan bawanka Yesse ne, na Betlehem.”

  15. 1 Sama’ila 18:1kusan 1063 K.H.

    Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.

  16. 1 Sama’ila 18:2kusan 1063 K.H.

    Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba.

  17. 1 Sama’ila 18:3kusan 1063 K.H.

    Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.

  18. 1 Sama’ila 18:4kusan 1063 K.H.

    Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.

  19. 1 Sama’ila 18:5kusan 1063 K.H.

    Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.

  20. 1 Sama’ila 18:6kusan 1063 K.H.

    Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.

  21. 1 Sama’ila 18:7kusan 1063 K.H.

    Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

  22. 1 Sama’ila 18:8kusan 1063 K.H.

    Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”

  23. 1 Sama’ila 18:9kusan 1063 K.H.

    Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.

  24. 1 Sama’ila 18:10kusan 1063 K.H.

    Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.

  25. 1 Sama’ila 18:11kusan 1063 K.H.

    Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.