Tsallake zuwa abun ciki

circa 1050–1010 BC

Samuel & King Saul

Israel demands a king; Samuel anoints Saul, whose disobedience leads to his rejection as God chooses a man after his own heart.

810 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. 1 Sama’ila 23:28kusan 1061 K.H.

    Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.

  2. 1 Sama’ila 23:29kusan 1061 K.H.

    Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.

  3. 1 Sama’ila 24:1kusan 1061 K.H.

    Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.”

  4. 1 Sama’ila 24:2kusan 1061 K.H.

    Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.

  5. 1 Sama’ila 24:3kusan 1061 K.H.

    Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon.

  6. 1 Sama’ila 24:4kusan 1061 K.H.

    Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.

  7. 1 Sama’ila 24:5kusan 1061 K.H.

    Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu.

  8. 1 Sama’ila 24:6kusan 1061 K.H.

    Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.”

  9. 1 Sama’ila 24:7kusan 1061 K.H.

    Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.

  10. 1 Sama’ila 24:8kusan 1061 K.H.

    Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  11. 1 Sama’ila 24:9kusan 1061 K.H.

    Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’?

  12. 1 Sama’ila 24:10kusan 1061 K.H.

    Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’

  13. 1 Sama’ila 24:11kusan 1061 K.H.

    Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina.

  14. 1 Sama’ila 24:12kusan 1061 K.H.

    Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba.

  15. 1 Sama’ila 24:13kusan 1061 K.H.

    Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.

  16. 1 Sama’ila 24:14kusan 1061 K.H.

    “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo?

  17. 1 Sama’ila 24:15kusan 1061 K.H.

    Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.”

  18. 1 Sama’ila 24:16kusan 1061 K.H.

    Da Dawuda ya gama wannan magana, sai Shawulu ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Sai ya fasa da kuka.

  19. 1 Sama’ila 24:17kusan 1061 K.H.

    Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.

  20. 1 Sama’ila 24:18kusan 1061 K.H.

    Ga shi yanzu ka faɗa mini alherin da ka yi mini. Ubangiji ya bashe ni a hannunka amma ba ka kashe ni ba.

  21. 1 Sama’ila 24:19kusan 1061 K.H.

    In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau.

  22. 1 Sama’ila 24:20kusan 1061 K.H.

    Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka.

  23. 1 Sama’ila 24:21kusan 1061 K.H.

    Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.”

  24. 1 Sama’ila 24:22kusan 1061 K.H.

    Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya.

  25. 1 Sama’ila 25:1kusan 1060 K.H.

    Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.