Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Watchfulness

167 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

  2. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

  3. Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.

  4. ’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;

  5. waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;

  6. masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.

  7. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  8. Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!

  9. Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin.

  10. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

  11. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.

  12. ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.

  13. Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.

  14. A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

  15. Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki.

  16. Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

  17. Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.

  18. Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.

  19. Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.

  20. Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.

  21. Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.

  22. amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,

  23. Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.

  24. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.

  25. Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce.