Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tyre

113 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Za su tā da muryarsu su yi kuka mai zafi a kanki; za su yayyafa ƙura a kawunansu, su yi ta birgima a cikin toka.

  2. Za su aske kawunansu saboda ke za su kuma sa tufafin makoki. Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai da kuma kuka mai zafi.

  3. Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?”

  4. Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya.

  5. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke.

  6. Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.

  7. ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

  8. “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Cikin alfarmar zuciyarka ka ce, “Ni allah ne; ina zama a kan kursiyin allah a tsakiyar tekuna.” Amma kai mutum ne ba allah ba, ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.

  9. Ka fi Daniyel hikima ne? Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?

  10. Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka.

  11. Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma.

  12. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah,

  13. zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.

  14. Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna.

  15. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.

  16. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.

  17. “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba.

  18. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa.

  19. Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  20. “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku.

  21. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku.

  22. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.

  23. “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu.

  24. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.

  25. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,