Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tyre

113 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.

  2. Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.

  3. Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta.

  4. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.

  5. “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.

  6. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

  7. Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.

  8. Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.

  9. Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.

  10. Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku,

  11. Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.

  12. Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.

  13. Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.