- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Solomon: Is visited by the queen of Sheba
Ayoyi game da Is visited by the queen of Sheba
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.
Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta.
Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata.
Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina.
Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.
Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne.
Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.”
Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba.
(Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja.
Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.)
Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta.
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.
Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata.
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina,
ta ga abincin da yake teburinsa, ta ga zaman fadawansa, bayi masu yin masa hidima cikin rigunansu, ta ga masu riƙe kwaf cikin rigunansu da kuma hadayun ƙonawar da ya yi a haikalin Ubangiji, sai mamaki ya kama ta.
Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da nasarorinka da hikimarka, gaskiya ne.
Amma ban gaskata abin da suka faɗa ba sai da na zo na kuma gani da idanuna. Tabbatacce, ko rabin girman hikimarka ba a faɗa mini ba, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.”
Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba.
(Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja.
Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.)
Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya.